SIRRIN GIRKI
Sirrikan Girki guda goma wadanda kowacce mace yakamata ta san su
1.IDAN ZAKIYI AMFANI DA TUMATIR NA GONGONI KO LEDA WAJEN YIN STEW KADA KIBARSHI YA DADE A WUTA
2.IDAN ZAKIYI AMFANI DA TAFARNUWA A GIRKINKI KISOYA BAZAI SA WARIN BAKI KO YA RINKA FITA A NUMFASHI BA, IDAN SON SAMU NE MA KI RINKA SOYASHI TAREDA ALBASA
3.IDAN ZAKIYI AMFANI DA KAYAN LAMBU (VEGETABLES) KAMARSU CARROT DA GREEN PEPPER KO ALAYYAHU KIBARSHI SAIKIN GAMA GIRKIN KISAKA AKARSHE IDAN KUMA TUKUNYANKI NA RIKE ZAFI KARKISAKA SAIKIN SAUKE KISAKA KIRUFE TUKUNYAR YAYI KAMAN MINTI 5 ZAKIGA YAFI BADA COLOUR MAI KYAU SANNAN YAFI AMFANI A JIKI
4.IDAN KIKAYI MIYA KIBARSHI A TUKUNYA YAYI KAMAN MINTI 30 KO AWA DAYA ZAKIGA YAFI KYAU DA DANDANO ESPECIALLY IDAN MIYAN STEW NE KO FRIED VEGETABLE
5.IDAN ZAKIYI AMFANI DA MANJA KIFARA SOYA KAYAN MIYANKI DA MANGYADA IDAN ZAKISA KANWA KIBARI SAI KIN GAMA HADA KOMAI KIN KUSA SAUKEWA SAI KISA MANJAN ZAKIGA YAFI FITOWA DA DANDANO
6.IDAN ZAKI DAFA KIFI KISOYASHI ANA GOBE ZAA ACI, SAIKIN BADA LABARI
7.IDAN ZAKI DAFA GANDA KO KAYAN CIKI KI WANKESU DA RUWAN KHAL SANNAN KIDAFA SAKIGA YANUNA CIKIN SAUKI BABU GARDAMA
8.KIYI AMFANI DA TOKAN MIYA MAIMAKON KANWA ESPECIALLY IDAN ZAKIYI STEW KO FRIED VEGETABLES ZAKIGA COLOUR YAFITO SOSAI YAYI KYAU BAKAMAN YADDA KANWA KESASHI DUHU BA
9.IDAN ZAKIYI KOSAI KADA KISA MAGGI KISA GISHIRI DA KAFI ZABUWA IDAN KINA AMFANI DASHI SANNAN KI FASA KWAI ACIKI ZAKIGA YATASHI YAYI KYAU SABODA MAGGI NA SAKASHI DUHU KUMA YA RINKA SHAN MAI SAIKIGA DA ANCI KADAN YA GINSHI MUTUM
10.IDAN ZAKIYI BLACK TEA KITAFASA TEA DA DARE KISA KAYAN KAMSHI A FLASK SAIKI JUYE TEA AKAI WASHEGARI DASAFE KISA SUGAR KISAKE TAFASAWA ZAKIJI KAMSHINSHI DABANNE
Comments
Post a Comment